AFIRKA
2 minti karatu
Dakarun RSF sun kai hari kan wani masallaci da 'yan gudun hijira ke samun mafaka, mutum 13 sun rasu
Wani wanda ya shaida lamarin ya ce kusan mutum 70 ne ke samun mafaka a cikin masallacin bayan dakarun na RSF sun shiga gidajensu.
Dakarun RSF sun kai hari kan wani masallaci da 'yan gudun hijira ke samun mafaka, mutum 13 sun rasu
Dakarun RSF / Others
9 Oktoba 2025

Harin makaman atilari da dakarun RSF na Sudan suka kai ya yi sanadin mutuwar mutum 13 a cikin wani masallaci a birnin El-Fasher da ke cikin mawuyacin hali, kamar yadda shaidu biyu suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP a ranar Alhamis.

“Bayan harin da aka kai da rana, mun ciro gawawwaki 13 daga ƙaƙashin baraguzan ginin kuma muka binne su,” kamar yadda wani mazaunin yankin ya yi bayani game da harin da aka kai a ranar Laraba.

Wani wanda ya tsira daga harin ya ce: “Mun kasance iyalai 70 a cikin masallacin bayan ‘yan RSF sun shiga gidajenmu. Jiya, harsasai na makaman atilari sun rinƙa faɗowa, inda suka kashe mutane 13 daga cikinmu, suka raunata 20, kuma suka lalata wani ɓangare na masallacin.”

Harin ya zo ne kwana guda bayan sojojin Sudan sun bayyana cewa sun ƙwace wurare da dama da dakarun RSF ɗin ke rike da su a El-Fasher.

Ƙawanyar RSF

Sojojin sun kama wasu motocin yaƙi da dama, ba tare da bayar da adadi ba, kuma sun lalata guda shida, ciki har da motoci masu sulke, kamar yadda sojojin suka bayyana.

RSF ta yi wa El-Fasher ƙawanya tun daga ranar 10 ga Mayun 2024, duk da gargaɗin ƙasashen duniya game da haɗarin da ke fuskantar garin, wanda ke zama cibiyar ayyukan jin kai a jihohin biyar na Darfur.

A cikin watannin baya-bayan nan, yankunan da RSF ke iko da su sun ragu sosai a faɗin Sudan yayin da sojojin suka faɗaɗa nasarorin su na soja zuwa jihohin Khartoum, White Nile, da Kordofan ta Arewa.