AFIRKA
2 minti karatu
Burkina Faso ta ƙi karɓar mutanen da aka kora daga Amurka
Matakin na Burkina Faso ya zo ne a daidai lokacin da ofishin jakadancin Amurka da ke Ouagadougou babban birnin ƙasar ya dakatar da ayyukan biza, matakin da gwamnatin Traore ta kira ''bita-da-ƙulli''.
Burkina Faso ta ƙi karɓar mutanen da aka kora daga Amurka
Shugaban kasar Burkina Faso Ibrahim Taore / TRT Afrika Hausa
9 awanni baya

Burkina Faso ta ki ƙarɓar mutanen da aka kora daga Amurka, a wani mataki na watsi da ɗaya daga cikin manufofin Shugaba Donald Trump kan baƙin-haure.

Tun bayan komawar Trump Fadar White House, gwamnatinsa ta mayar da hankali wajen tura mutane zuwa ƙasashe marasa karfi, musamman ƙasashen da ba su da alaka da su, a wani ɓangare na ƙoƙarin yaki da baƙin-haure.

A cikin ‘yan kwanakin nan a Afirka, ƙasar Eswatini da Ghana da Rwanda da kuma Sudan ta Kudu duk sun amince da mutanen da aka kora daga Amurka.

Sai dai kuma da yammacin ranar Alhamis, Ministan Harkokin Wajen Burkina Faso ya bayyana cewa, ƙasarsa da ke yankin yammacin Afirka ta yi watsi da matakin da Washington ta ɗauka.

"Bisa ƙa'ida, wannan shawara da muka ɗauka ba ta dace ba a wancan lokacin, sannan ta saɓawa ƙa'idar mutunci na ɗan’adam," kamar yadda Karamoko Jean-Marie Traore ya bayyana ta gidan talabijin din.

Masu AlakaTRT Afrika - Ghana za ta karɓi ƙarin mutum 40 da za a kora daga Amurka

Martanin Amurka

Kafin matakin na Burkina Faso, ofishin jakadancin Amurka da ke Ouagadougou babban birnin ƙasar, ya sanar da dakatar da ayyukansa na ba da biza ga galibin mutanen da ke zaune a Burkina Faso.

A maimakon haka, a yanzu 'yan ƙasar za su samu biyan buƙata ne a Lome, babban birnin makwabciyar ƙasar Togo.

"Shin wannan wata hanya ce ta matsin lamba a garemu? Ko kuma bita-da-ƙulli ne? To ko ma mene ne ... Burkina Faso ƙasa ce mai daraja, kuma wurin zuwa, ba wurin koro mutane ba ne," in ji Karamoko Jean-Marie Traore.

Tun bayan karɓar mulki a shekarar 2022 shugaban ƙasar Burkina Faso, Kyaftin Ibrahim Traore, ya ɗaura ɗamarar ƙarfafa kyamar mulkin mallaka, tare da yin watsi da tsohuwar uwargijiyar ƙasar da ta yi mata mulkin mallaka wato Faransa da sauran kasashen yammacin duniya.