Aƙalla mutum 48 sun rasa rayukansu kuma fiye da 152 sun jikkata a rikicin da ya ɓarke tsakanin sojojin Sudan ta Kudu da dakarun 'yan adawa a wani gari da ke kan iyaka a arewa maso gabashin ƙasar, kamar yadda kafofin watsa labarai na cikin gida suka ruwaito a ranar Lahadi.
Rikicin ya fara ne a ranar Asabar a lokacin da dakarun Sudan People's Liberation Movement-in-Opposition (SPLM-IO) suka kai hari kan sansanin sojojin South Sudan People's Defense Forces (SSPDF) a Burebiey, wani gari da ke kan iyakar Sudan ta Kudu da Habasha a gundumar Nasir da ke Jihar Upper Nile, kamar yadda Gwamna James Koang ya shaida wa gidan rediyon Eye Radio a ƙasar.
Gwamnan ya ce, bisa ga rahotannin da suka samu, fiye da mutane 48 daga cikin dakarun SPLM-IO da mayaƙan White Army da ke goyon bayansu sun rasu, yayin da fiye da 148 suka jikkata. A ɗayan ɓangaren kuma, SSPDF ba su yi asarar rai ba, sai dai sojoji huɗu sun jikkata.
Koang ya yi kira ga zaman lafiya tare da roƙon dakarun 'yan adawa su dakatar da hare-haren da suke kai wa SSPDF.
'Muna nan don zaman lafiya'
“Muna goyon bayan zaman lafiya, kuma idan wani yana son magana da mu, muna nan a shirye,” in ji shi.
Sudan ta Kudu ta samu 'yancin kai daga Sudan a shekarar 2011, amma bayan shekaru biyu ta faɗa cikin yaƙin basasa.
Aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya ta shekarar 2018 ta kasance cikin jan ƙafa, kuma kwanan nan an samu ƙarin tashin hankali bayan rikici mai tsanani tsakanin mayaƙan White Army, wata ƙungiyar 'yan tawaye da ake cewa suna goyon bayan Mataimakin Shugaban Kasa na Farko Riek Machar, shugaban babbar jam'iyyar adawa SPLM-IO, da SSPDF a gundumar Nasir, Jihar Upper Nile da ke arewa maso gabas.
A watan Maris, Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir Mayardit ya yi wa Machar da ‘yan ƙungiyarsa ɗaurin talala, bayan rikicin da ya ɓarke tsakanin mayaƙan White Army da sojojin gwamnati a Jihar Upper Nile.
A ranar 11 ga Satumba, Kiir ya dakatar da Machar da Ministan Man Fetur Puot Kang Chol, a wannan rana kuma Ministan Shari'a ya tuhume su da laifuka da dama, ciki har da cin amanar ƙasa da kisan kai, sai dai Machar ya musanta zargin.