| hausa
AFIRKA
3 minti karatu
Ruftawar mahaƙar ma’adanai ta yi ajalin aƙalla mutum 32 a DRC
Wata gada ta rufta a wata mahaƙar ma'adinai na kobolt a kudu maso gabashin Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo inda ta kashe aƙalla masu haƙar ma’adinai 32, kamar yadda wani jami’in gwamnati a yankin ya bayyana ranar Lahadi.
Ruftawar mahaƙar ma’adanai ta yi ajalin aƙalla mutum 32 a DRC
Masu haƙar ma'adinai da hannu yayin da suke aiki a Tilwezembe a wajen Kolwezi
17 Nuwamba 2025

Wata gada ta rufta a wata mahaƙar ma’adinai a kudu maso gabashin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo, lamarin da ya yi ajalin aƙalla masu haƙar ma’adinai 32, kamar yadda wani jami’in gwamnati na yanki ya bayyana ranar Lahadi.

Gadar ta faɗo kan wani wurin da ruwa ya taru ne a wata mahaƙar ma’adinai ranar Asabar a lardin Lualaba, kamar yadda Roy Kaumba Mayonde, Ministan Tsaron Cikin Gida na lardin, ya shaida wa manema labarai. Ya ce an samo gawarwaki 32 kuma ana neman ƙarin gawarwaki.

Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo ce take samar da sama da kashi 70 cikin 100 na kobolt a duniya, wani abU da ke da muhimmanci wajen haɗa baturan da ake amfani da su cikin motoci na laturoni da komfutar tafi da gidanka da wayoyin salula .

Fiye da mutum 200,000 ne aka yi ƙiyasin cewa suna aiki wata babbar mahaƙar ma’adinai ta kobolt a ƙasar da ke tsakiyar Afirka.

Haramta haƙar ma’adinai ba bisa ƙ’ida ba

Hukumomin ƙasar sun ce gadar ta rufta ne a mahaƙar ma’adinai ta Kalando, a wani wuri dake da nisan kimanin kilomita 42 da babban birnin lardin Lualaba da ke kudu maso gabashin ƙasar.

"Duk da cewa an haramta zuwa mahaƙar a hukumance saboda ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da kuma barazanar zaftarewar ƙasa, masu haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba suna kutsawa cikin mahaƙar," a cewar Mayonde.

Ya ce yadda masu haƙar ma’adinan suke dannawa kan gadar ta wucin gadi da aka yi domin tsallake ramin da ke cike da ruwa ne ya sa gadar ta rufta.

Wani rahoton SAEMAPE, wata hukumar gwamnati mai sa ido da kuma taimaka wa ƙungiyoyin haɗin gwiwa, ya ce zuwan sojoji mahaƙar ma’adinan ta Kalando ya sa mutane sun gigice.

Tsohuwar jayayya

Rahoton ya ce mahaƙar ma’aidanan ta kasance wacce ake jayayya a kanta da aka daɗe ana yi tsakanin masu haƙar ma’adani, wata ƙungiyar haɗin gwiwa da aka kafa domin tsara tono a wurin, da kuma waɗanda suke da izini a hukumance na jan ragamar wurin, waɗanda aka ce suna da alaƙa ‘yan China.

Masu haƙar ma’adanai da suka faɗa "sun ringa faɗawa kan juna, lamarin da ya janyo mace-mace da rauni," in ji rahoton.

Hotunan da ofishin lardi na hukumar kare haƙƙin ɗan’adam na ƙasar (CNDH) ya tura wa kamfanin dillancin labaran AFP ya nuna masu haƙar ma’adanai suna tono gawawwaki daga cikin ramin inda aka ga aƙalla gawagarwaki 17 suna kwance a ƙasa kusa da wurin.

Jami’in da ke jagorantar hukumar CNDH a yankin Arthur Kabulo ya shaida wa AFP cewa masu haƙar ma’aidanai ba bisa ƙa’ida fiye da 10,000 suke aiki a mahaƙar ma’adanan Kalando. Hukumomin yankin sun dakatar da ayyuka a wurin ranar Lahadi.

Arzikin ma’adanan DRC ya kasance silar wani rikicin da ya shafe fiye da shekara talatin yana addabar gabashin ƙasar.

 

Rumbun Labarai
Ghana za ta tura injiniyoyin soji don taimakawa wajen sake gina Jamaica bayan afkuwar guguwa
Mutane 70 sun ɓace bayan jirgin ruwa ɗauke da mutum 120 ya kife a DRC
Wata ƙungiya ta zargi kamfanin Nestle da sayar wa Afirka abincin jarirai mai sikari da yawa
Ranar Makewayi ta Duniya: Kundin tsafta na Afirka don inganta lafiya da mutunci
Sabon Alƙalin Alƙalan Ghana Baffoe-Bonnie ya fara aiki
An raba fiye da mutum 100,000 da gidajensu a Al Fasher na Sudan daga lokacin da RSF ta ƙwace birnin
Kafafen watsa labaran Afirka: Abokan kawo ci gaba da ake mantawa da su
Za a ƙara farashin man fetur a Ghana
An samu rahotanni 32 na yi wa 'yan mata fyade bayan RSF ta ƙwace birnin Al Fasher - Likitoci
Mutum huɗu sun rasu bayan jiragen ruwa biyu na 'yan ci-rani sun kife a gaɓar tekun Libya
DR Congo da M23 sun cim ma yarjejeniyar zaman lafiya 'ta tarihi' a Qatar
AfDB zai ba Nijar CFA biliyan 98.7 domin magance matsalar ruwa ta shekara 70 a Zinder
MDD ta yi gargaɗi kan ƙazancewar yaƙin Sudan, ta yi kira kan barin shigar da kayan agaji
An gabatar da GH¢302bn a matsayin kasafin kuɗin Ghana na 2026 ga majalisar dokokin ƙasar
Sojojin Sudan sun daƙile harin RSF kan filin jirgin sama da dam a arewacin ƙasar
Rubio ya nemi a daina bai wa RSF makamai, ya ɗora wa rundunar laifi kan kashe-kashe a Al Fasher
Dalilin da ya sa TikTok ya goge bidiyoyi miliyan 1.5 da 'yan Uganda suka wallafa
Mutum 12 sun mutu a turmutsutsun neman aikin soja a Ghana – Rahotanni
Mahaucin Al Fasher: Yadda hotonsa ya zama alamar bakin cikin Sudan
UN Women: Mata da 'yan mata 11M suna fama da matsanancin ƙarancin abinci a Sudan sakamakon yaƙi