Ana neman kusan mutane 70 bayan wani jirgin ruwa ya kife a wani kogi a lardin Kasai, a tsakiyar Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo, in ji kafofin watsa labarai na yankin a ranar Laraba.
Jirgin yana kan hanyarsa ta zuwa babban birnin kasar Kinshasa daga tashar Bena Dibele, da ke da nisan fiye da kilomita 800, lokacin da ya nutse a ranar Litinin a kogin Sankuru, sakamakon guguwa, a cewar gidan rediyon Majalisar Dinkin Duniya.
“Jirgin yana ɗauke da kimanin mutane 120. An ceto kimanin 50 zuwa yanzu, kuma ana ci gaba da ayyukan neman waɗanda ba a same su ba,” in ji wani jami’in yankin Francois Ahoka.
Ahoka ya bayyana ƙalubalen da ƙungiyoyin ceto suka fuskanta, kuma ya yi kira ga iyalai da su ci gaba da tuntuɓar hukumomin yankin don taimakawa wajen tantance waɗanda aka ceto da gawawwakin wadanda suka mutu.
Ana yawan amfani da hanyoyin sufurin ruwa a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo saboda mafi yawan titunan ƙasar ba su da kyau.

















