Ofishin jakadancin China a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ya gargaɗi ‘yan kasar da su kauce wa yin aiki a masana’antu masu tsananin haɗari, kamar wuraren haƙar zinari, yana cewa za su iya zama “bayin haƙar ma’adinai.”
A wata sanarwa da ofishin ya fitar a ranar Alhamis, ya ce ‘yan China da suke harkar haƙar ma’adinai a ƙasashen Afirka a ‘yan shekarun nan sun fuskanci matsalolin tsaro ko “sun fuskanci gagarumin haɗari na tsaro.”
Yayin da wasu daga cikinsu suka fuskanci asarar kuɗaɗe saboda tarar da aka ɗaura musu ko zuba jarin da ya durƙushe, wasu sun fuskanci barazanar cin zarafi, a cewar sanarwar, tana cewa an kwace wa wasu daga cikinsu takardu, inda aka mayar da su “bayin hakar ma’adinai.”
“Kungiyoyi masu adawa da gwamnati da ke ɗaukan makamai sun kai wa wasu hari an kashe su, wasu kuma faɗa tsakanin ɓangarorin gwamnati da ƙungiyoyi da dama ya rutsa da su, wasu kuma sun mutu saboda munanan cutuka kamar zazzabin cizon sauro,” a cewar sanarwar.
Ta kuma yi gargaɗin cewa an kashe wasu ko an jikkata su a haɗarorin mota “da aka tsara” ko “rataya” saboda saɓani da ya biyo bayan rikinci da wasu masu ruwa da tsaki.
“Kada ku je wuraren da suke da haɗari a wajen Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya don yin aiki, sannan ku kauce wa masana’antu masu haɗari kamar wuraren haƙar zinari,” a cewar sanarwar ta ofishin jakadancin, yana kiran waɗanda suka riga suka shiga su dakata nan take, sannan su kai kansu ofishin jakadancin.

















