Ranar Makewayi ta Duniya na iya zama kamar wata alama a kalandar abubuwan da suke faruwa a duniyar da take a cike, har sai kun fuskanci gaskiyar cewa har yanzu mutane biliyan 3.5 na rayuwa ba tare da bandaki mai tsafta ba.
Shirun da ke tattare da tsafta wani ɓangare ne na rashin kulawa, kuma galibi akwai sakaci.
Amma gaskiyar ita ce, wannan batu mara daɗi yana bayyana ko yara kanana na tsira daga kamuwa daga cututtuka, ko mata za su iya kula da jinin al'ada cikin mutunci, da kuma yuwuwar al'ummomi gaba ɗaya su tsira daga yawaitar kamuwa da cututtukan da za a iya hana su bulla.
A Afirka, yanayin da ake ciki na dauke da bambance-bambance. Yayin da wasu ƙasashe suka cim ma nasarar kare lafiyar jama'a, wasu kuma suna cikin mawuyacin hali inda yawancin al'ummarsu ba su da kayan amfanin rayuwa na yau da kullum da ake bukata.
Ya zuwa wannan lokaci, batun tsaftar makewayi a nahiyar ya kasance mai gibi. Amma wadansu ‘yan ƙasashe a yanzu suna sake rubuta wannan labari kuma suna nuna cewa ci gaba yana yiwuwa tare da aniya da kudiri na siyasa, kirkire-kirkire da haɗin gwiwar al'umma.
A cewar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da Shirin Kula da Ruwa, Tsaftar Muhalli da Tsaftar Jiki na UNICEF, wani babban mataki ya bayyana a Afirka.
Samar da sharudda
Babban yankin da ke kan gaba a wannan fanni shi ne tsibiran Seychelles na Tekun India. Tare da kusan kashi 98% na damar samun tsaftataccen muhalli cikin aminci da tsafta, kasar ta zama zakaran gwajin dafi na duniya a nahiyar.
A Seychelles, tsafta ba wai kawai game da bandakuna ba ne; ya kunshi samar da ingantaccen tsarin da ake kula da shara da zubar da ita cikin aminci, wanda hake ke bayar da kariya ga mutane da muhallan tsibirin.
Tare da sama da kashi 90% na damar samun tsaftataccen muhalli cikin aminci, Tunisiya ta fito a matsayin wata babbar majagora.
Tsarin da gwamnati ta dabbaka na tsawon shekaru da dama, wanda aka gina tare da Hukumar Kula da Tsabtace Ruwa ta Ƙasa, wanda aka kafa a shekarar 1974, ya taimaka wajen tsarawa da kuma kula da kayayyakin more rayuwa da ke daukar ruwan makewayi.
Manufar ita ce a haɗa birane da garuruwa a duk faɗin ƙasar zuwa hanya guda ta gama gari.
Da yake Tunisia ta fahimci cewa makewayi yana da tsafta kamar tsarin da ke kula da ruwan da yake fitarwa, ta zuba jari sosai a masana'antun tace ruwa sama da 120 kuma ta zama jagora a yankin wajen sake amfani da ruwan, inda take sake amfani da kashi 30% na ruwan bandakuna don ban ruwa ga gonaki.
Duk da cewa kokarin ya game kusan dukkan birane inda ya zama ruwan dare, shirye-shiryen da aka yi niyyar aiwatarwa sun faɗaɗa wuraren tsaftace muhalli sosai a yankunan karkara kuma sun rufe gibin da ke tsakanin karkara da birane.
Mauritius ta cim ma irin wannan sakamako ta hanyar haɗa kayan aiki da kirkire-kirkire. Hukumar Kula da Ruwan Bandakuna ta ƙasar ta ci gaba da faɗaɗa hanyoyin gudanar ruwa mai najasa, musamman a yankunan bakin teku masu yawan jama'a inda tsafta ke da mahimmanci ga bunkasar masana'antar yawon buɗe ido ta ƙasar.
Daukar matakan riga-kafi don magance matsalar muhalli nan take, ciki har da gangamin neman mayar da tsaffin tankunan tsabtace muhalli zuwa wuraren tsaftace muhalli da haɗa su da hanyar gudanar ruwan bandakuna ta kasa, wanda hakan ke jagorantar shirin. Dole ne aiki da dokokin.
A ƙasar Mauritius, manyan ƙa'idojin da aka saka sun bukaci ɓangaren yawon buɗe ido da ya samar da wani muhimmin abu na tattalin arziki ga tsafta, wanda ke haifar da saka hannun jari a fasahar zamani ta kula da ruwan da ke fito wa daga bandakuna da kashe shara, wanda hakan zai kuma daga martabar kasar.
Matsalar rashin kayan aiki a wasu kasashen
Nasarar da Seychelles, Tunisia da Mauritius suka samu wajen kafa ka'idojin tsaftar muhalli sun zama matsalolin da wasu kasashen ke fuskanta.
Shirin Haɗin Gwiwa na UNICEF ya bayyana yankin kudu da hamadar Sahara a matsayin cibiyar matsalar tsaftar muhalli ta duniya. A waɗannan ƙasashe da yawa, makewayi mai tsafta da nagarta ba su isa ga yawancin jama'a.
Kasashen Tsakiya da Gabashin Afirka na da misalai marasa dadin ji. Kusan kashi 21% na al'ummar Chadi ne ke da damar samun tsaftataccen muhalli. Yin bayan gida a fili abu ne da ya zama ruwan dare a kasar.
Ethiopia, ɗaya daga cikin ƙasashe mafi saurin bunƙasa a nahiyar Afirka, na da munanan alkaluma kan samun muhalli mai tsafta da kashi 27%, wanda ya bar miliyoyin mutane suna fuskantar cututtukan da za a iya hana kamu da su.
Sudan ta Kudu, wacce ke fama da rikici da rashin ci gaba na tsawon lokaci, ta zama wurin da ake samun barkewar cututtuka waɗanda za a iya kauce musu ta hanyar tsaftace muhalli yadda ya kamata.
A Nijar da Madagascar, inda samun tsaftataccen muhalli ya kai kusan kashi 30%, rabambanci tsakanin ƙauyuka da birane a bayyane yake karara, kuma tsarin kula da lafiya mai rauni ya kai wani mataki mai ban tsoro.
Masana sun bayyana gibin tsafta ba wai kawai a matsayin karancin kayayyakin more rayuwa ba, har ma a matsayin bukatar gaggawa ta jinkai, wanda ke haifar da mutuwar yara sakamakon cutar gudawa, yana kara ta'azzara rashin abinci mai gina jiki, kuma yana gurbata muhalli.
Duba ga sama da hanyoyin fitar da ruwan makewayi
Bambancin da ke tsakanin shugabannin Afirka da waɗanda aka bari a baya na bayyana yadda abin yake.
Nasarorin da Seychelles, Tunisia da Mauritius suka samu sun dogara ne akan aniyar shugabanci wadda ta ɗauki tsafta a matsayin fifikon ƙasa, wanda ke samun goyon bayan kuɗaɗen shiga da ƙa'idodi masu dorewa.
Fifikon tsafta ya taimaka wajen gina kashin bayan da ba a iya gani ba - kan hanyoyin magudanar ruwa da wuraren tace ruwa - wanda ke kare lafiyar jama'a kowace rana a hankali.
A yankunan karkara, hanyoyin tsaftace muhalli masu araha da amfani na tabbatar da cewa babu wata al'umma da aka bari a baya.
Wannan bambanci tsakanin waɗanda ke jagoranci da waɗanda ke fafutukar cim ma burinsu yana ba da taswirar hanya ga wasu da ke tafe.
Ƙasashe kamar Ghana, Senegal da Rwanda tuni suka fara tafiya a wannan hanyar, suna aiwatar da shirye-shiryen ƙasa masu girma waɗanda ke nuna cewa ci gaba cikin hanzari na nan tafe.

















