Shugaban Ghana John Dramani Mahama ya yi shelar shirye-shiryen tura mambobin rudununar injiniyoyin sojin Ghana na runduna ta 48 zuwa Jamaica domin tallafa wa ƙoƙarin sake gina ƙasar bayan lalata ababuwan da guguwar Hurricane Melissa ta yi.
Shugaba Mahama, da yake magana ranar Laraba yayin bikin tunawa da taron fafatukar kare baƙaƙen fata na biyar karo na 80, ya ce rundunar da ta soji ta ƙunshi sojoji masu ƙarewa a harkar injiniya na soji da na farar hula za ta taimaka wajen gina gidaje na wucen gadi wa ‘yan Jamaica da suka rsa gidajensu.
“Daga cikin waɗanda suka fi ba da ƙarin gwiwa na kishin Afirka da Ghana, mun yanke shawarar haɗa abinci da sauran abubuwa domin mu tura su ga ‘yan’uwanmu a Jamaica da Cuba," kamar yadda Mahama ya sanar da mahalarta taron.
Ana tsammanin tawagar ta ƙunshi injiniyoyi da mesin da kafintoci da sauran masu ƙwarewa a fasaha, kamar yadda kamfanin dillancin labaran ƙasar ya ruwaito.
Tallafin Nahiya
Mahama ya kuma yi amfani damar taron wajen kira ga ƙasashen Afirka da su miƙa taimakonsu zuwa Jamaica da Cuba, waɗanda masifar guguwar ta shafa, musamman bayan an samu kira kai-tsaye daga Firaministan Jamaica Holness.
"Kuma saboda haka, idan za ka iya kira ga ‘yan’uwanmu ‘yan Afirka da su taimaka mana, yawan ta’adin da aka samu a Jamaica ya fi ƙarfin abin da za mu iya gyarawa mu kaɗai," kamar yadda Shugaba Mahama ya ambato Firaministan Jamaica Andrew Holness yana cewa.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Ghana ta ce ta riga ta bayyana wa Ƙungiyar Tarayyar Afirka lamarin, tana mai kira ga ƙasashe mambobin ƙungiyar su ba da gudnumawar abin da za su iya wajen taimakawa domin samar da muhalli na wucin gadi.
Guguwar Hurricane Melissa, ɗaya ce daga cikin guguwa mafi ƙarfi da aka taɓa samu a tarihi a Tekun Atilantika, ta yi ɗaɗɗaya da yankin yammacin Jamaica ranar 28 ga watan Oktoba inda ta dira a Gabashin Cuba kuma ta lalata gidaje da amfanin gona.
Firaministan Andrew Holness ya ce aƙalla mutum 50 sun mutu kuma ya kiyasta cewa darajar ababuwan da suka lalace sun kai dala biliyan shida zuwa biliyan bakwai.
Mahama ya ce Ghana ta riga ta tura wasu kayayyakin agaji zuwa Jamaica.

















