An kama wani matashi ɗan Mohammed Yusuf, wanda ya kafa Boko Haram, a ƙasar Chadi, inda ake zargin yana jagorantar wata ƙungiyar ta'addanci, kamar yadda wata majiya ta leƙen asiri da tsohon mamban Boko Haram ta tabbatar.
An kama matashin mai suna Mohammed Yusuf tare da wasu mutane biyar da ake zargin mambobin ƙungiyar ta'addanci ne, wadda aka kafa a Nijeriya, ƙasar da ke makwabtaka da Chadi, shekaru kaɗan kafin haihuwarsa.
Mahaifinsa, Mohammed Yusuf, shi ne wanda ya kafa wannan ƙungiyar ta'addancin.
Boko Haram ta shafe kusan shekaru 15 tana haddasa matsalolin tsoro a yankin Tafkin Chadi, tare da kai hare-hare masu tsanani kan ƙauyuka da sansanonin sojoji a 'yan watannin nan.
Rundunar ‘yan sandan Chadi ta tabbatar da kama mutane shida da ake zargin mambobin Boko Haram ne, amma ba ta tabbatar ko ɗaya daga cikinsu ɗan Mohammed Yusuf ba na.
Matashi ɗan ta’adda
Wata majiya daga fannin leƙen asiri na Nijeriya da ke yankin Tafkin Chadi ta shaida wa AFP a ƙarshen mako cewa sun samu rahoton kama wata ƙungiyar ta'addanci mai mutum shida a Chadi.
"Ƙungiyar tana ƙarƙashin jagorancin Yusuf, ƙaramin ɗan marigayi wanda ya kafa Boko Haram," in ji majiyar.
Sai dai majiyar ta ce wannan ƙungiyar ta'addanci ta rabu da Boko Haram saboda saɓani kan aƙida.
Majiyar ta ƙara da cewa Yusuf yana ƙarami lokacin da aka kashe mahaifinsa a shekarar 2009, yayin wani farmakin soji kan Boko Haram, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane kusan 800, inda ta bayyana shekarunsa a yanzu da 18.
‘Yan fashin daji
Hotunan da AFP ta gani bayan kama su a Chadi sun nuna wani matashi mai kama da Muhammed Yusuf tsaye kusa da wasu da suka girme shi.
"Jami'an tsaron Chadi ne suka kama shi da ƙungiyarsa. Mutum shida ne gabaɗaya," in ji majiyar da ta gaya wa AFP.
Rundunar ‘yan sandan Chadi ta bayyana cewa sun kama "'yan ta'adda da ke aiki a cikin birni... ba su da takardun izinin zama, kuma mambobin Boko Haram ne," in ji kakakin ‘yan sanda Paul Manga na birnin N'Djamena.
Ya ce an kama gungun ne "watanni kaɗan da suka gabata."
Cibiyar yaƙi da ta'addanci ta Nijeriya da hukumar leƙen asiri ta ƙasa ba su amsa tambayoyin da AFP ta yi musu ba nan-take.